Kungiyar ‘yan Jaridun Online ta Jihar Kano ya taya Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa murnar nadin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Singh ya masa a matsayin Mai magana da yawunsa.
Wannan na cikin wata sanarwar Mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Alhaji Yakubu Salisu.
Ta cikin sanarwar, Alhaji Yakubu ya ce, matsayin da gwamnan ya bai wa Bature ya dace da wajen sosai, kasancewa gogagge a fannin Jarida.
“Muna alfari da nadin da aka yiwa dan uwa abokin aiki, sakamakon jajircewa da nuna himma a fannin aikin a Koda yaushe”
Alhaji Yakubu.
“Ina da tabbacin cewa Sunusi Bature zai gudanar da aikinsa tare sauran Yan Jaridun Jihar Kano, da nufin ci Yar JIhar gaba ta fannoni da dama” Alhaji Yakubu