Hausa

Ku Dakata: Bana Son Sa Toka-Sa-Katsi A Tsakanin Hukumomi A Gwamnati Na

Aisha Muhammad
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bukaci rundunar tsaron farin kaya ta DSS, da su bar ofishin hukumar EFCC reshen Jihar Lagos da nufin Kara inganta tsaro.
Wannan na cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun mataimakinsa kan kafafen yada labarai Mista Tunde Rahman.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da Jami’an tsaron DSS suka dirarwa ofishin hukumar EFCC da ke Ikoyin don tada zaune tsaye.
“Lokaci ya yi da ya kamata rundunar tsaro ta DSS, su bar ofishin hukumar  EFCC don ba su  damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata” Tinubu.
“Idan har da wata rashin jituwa a tsakanin ku, zan warwaresu nan da wasu lokuta da nufin kiyaye lafiya da dukiyoyin alummar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *