Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa, NUJ, ta taya Sunusi Bature Dawakin-Tofa murnar nadin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya masa, a matsayin Mai magana da yawunsa.
Wannan na cikin wata sanarwar Mai dauke da sa hannu Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Kwamrade Abbas Ibrahim da sakatarensa Abba Murtala.
Ta cikin sanarwar, Kwamrade Abbas ya ce, gwamnan ya zabi Wanda ya dace Kuma mai jajircewa wajen gudanar da aikinsa, ba dare ba rana.
Sanarwar ta Kuma ce, kungiyar NUJ, tana da yakinin cewa zai ci gaba da aikinsa bisa tsarin kundin aikin yan Jarida na kasa.
“Muna kira ga Yan Jaridun Jihar Kano da su kasance masu kare hakkokin Yan Jarida a aikinsu”.