Aisha Muhammad

 

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya nada malam Bala Ibrahim Mamser, a matsayin sabon Shugaban ma’iakatan gwamnatin Jihar.
Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun  Shugaban maiakatan Jihar Alhaji Husaini Ali Kila.
Ta cikin sanarwar, nadin zai fara aiki nan take.
Kafin nadin na shi, Alhaji Mamser tsohon kwamishinan yada labarai da matasa ne na Jihar Jigawa.
Ka zalika gwamnan ya Kuma nada sanata  Mustapha Makama Kiyawa a matsayin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar.
Sai Alhaji Adamu Muhammad Garun Gabas a matsayin Shugaban makarantu masu zaman kansu na jihar.
Sauran nade-naden sun hada da  Abdullahi S.G Shehu a matasyin babban akantan na  JIhar sai kuma  Dr. Habib Muhammad Ubale.

By News Room

Salim is a multimedia journalist with vast knowladge of content creation and production

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *