Hausa

Gwamnatin kano ta dau damarar yakar zazzabin cizon Sauro.

Aisha Muhammad.

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ta yi gargadi kan yadda cutar zazzabin cizon sauro ke ci gaba da kwarzabar mata masu juna biyu da kananan yara a Afirka.

An fitar da rahoton ne don tunawa tare da nuna irin illar da zazzabin cizan sauro ke jawowa, musamman ma ga kananan yara da mata masu juna biyu

Rahoton ya koka kan yadda aka karkace daga kokarin dakile mace-macen da cutar zazzabin cizon sauro ke haddasawa a duniya da kuma shirin yakarsa kan nan da shekara ta 2023.

Sai dai kuma a Jihar Kanon Nigeria, za’a iya cewa an dau saiti wajen magance wannan matsalar. Dan kuwa kimanin Yara milliyan Goma Sha biyu ne ake sa rai za su amfana da allurar Riga kafin cutar zazzabi n cizon sauro.

Gwamnatin JIhar Kano ce t bayyana hakan ta bakin Kwamishinan ma’aikatar Lafiya na Jihar Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa inda tace “za ta fara gangamin Yi wa Yara Yan kasa da shekaru biyar allurar riga kafi cutar zazzabin cizon sauro daga yau Talata”

Kwamishinan ya kara da cewa “Za a kwashe wattanni hudu, daga watan da muke ciki na Yuli zuwa watan Oktoba na shekarar da muke ciki, ana gudanar da aikin riga Kafin Mai taken gida gida ga alumma”

A cewarsa duba da irin illolin da sauro ke haifarwa ga alumma, yasa suka bullo da tsarin yin Rigakafin cutar gida-gida, Wanda hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta Ba da umarnin yin ta.

Haka nan kwamishinan ya ka ra da cewa “Mata masu juna biyu ma baza a barsu a baya ba, suma akwai nasu tsarin na rigakafin”

Da yake magana kan kudin da aka kashe kuwa ya kada baki yace “akalla an kashe sama da Naira million Dari takwas wajen magungunan gamida gidan sauro Mai magani, Wanda za a raba a watan Oktoba shekarar da muke ciki.

Ana sa ran gudanar da Allurar Rigakafin ne a fadin kananan hukumomin Jihar Arba’in da hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *