Uncategorized

Komai Ya Kammala Dan Rantsar Da Sabon Gwamnan Jihar Kano

Aisha Muhammad 

 

Gwamnatin Jihar Kano ta ce shirye shirye sun yi nisa don rantsar da zabbanen gwamnan Kano Injiniya Abba Yusuf a gobe Litinin.

Shugaban kwamitin karbar mulkin a Jamiyyar NNPP, Dr Baffa Bichi ne ya bayyana hakan a Wani Taron manema labarai da ya gudana a yau.
A cewar Bichi, za a rantsar da Gwamna Mai jiran gado da mataimakinsa a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Nan Kano.
” Gwamnatin Mai barin gado Bata ba mu hadin Kai daya kamata ba, kasancewa ita ya kamata ta shirya duk wasu shirye shirye rantsuwar bikin Amma abun ya gagara, inji Dr Bichi.
” An tanadi jamian tsaro da dama da nufin kare lafiyar zabbanen gwamnan da dukkannin wadanda za su hallarci rantsuwar bikin” A cewar Baffa Bichi.
Bichin ya Kuma ce akwai Baki na cikin gida Dana ketare da za su shigo Jihar Kano, domin hallartar taron rantsarwar na gwamnan Mai jiran gado Injiya Abba Yusuf, Abban Kanawa.
Ya Kuma ja hankula alumma da su Bada hadin ga Jamian da nufin inganta tsaron wajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *