News

Yadda Shirin AGILE Ya Ziyarci Karamar Hukumar Ajingi Dan Bunkasa Yanayin Shirin A Yankin

Aisha Garba Abubakar

Ranar Talata 20/02/2024 Shirin Kyautata Ilimin ‘Ya ‘ya Mata da Inganta Rayuwarsu ( AGILE ), takai ziyara dan ganin halin da shirin ke ciki a karamar hukumar Ajingi akan muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata.

Sadisu Idris Mataimakin mai kula da shirin na jihar Kano, yayi jawabin makasudin ziyarar tasu da kuma dalilan da shirin ya duba na rashin zuwan yara mata makaranta bayan tallafin da aka basu.

Halima Sadiya Tukur, daya daga cikin masu kula da shirin AGILE, tayi bayani kan shirin, na son ganin an inganta ilimin ‘ya’ya mata. Bincike ya nuna cewa jihar kano, na daya daga cikin jihohi da suke sahun baya a kasar nan wajen ilimin mata.

Halima, ta k’ara da cewa “wannan shiri akwai tsare tsare kashi kashi wanda shirin ya kunsa dan taimakawa wajan gyare gyaran makarantu, samar da mahallin karatu, samarda kayan koyo da koyarwa, da kayan koyar da sana’oi da bada tallafi ga masu sanaa da karatu ga yaran da suka fito daga gidajen da basu da karfin tattalin arziki.

Ta kara dacewa Akwai bangare nafarko wanda ze gina makarantu guda dari da talatin (130) ,A jahar kano, a kananun hukomomi Ashirin da Hudu wadanda sukeda karancin makarantu.

Karamar Hukumar Ajingi na daya daga cikin kananan hukumomin da zata amfana da shirin wanda ya kunshi gina kananan makarantun sikanditre guda Saba’in da Hudu a fadin jihar.

akawi manyan makarantu wato sikandire guda hamsin da biyar wanda karamar hukumar Ajingi tana daya daga cikin kananan hukomominda da zasu amfana. Shirin zai yi duba game da gyara gyare, da kuma bada tallafi domin yin wasu bukatu da makarantun suke bukata.

Hajiya Aisha Tijjani, daya daga cikin masu bada shawarwari akan shirin ajile,tayi kira ga iyaye dasu sauke hakkokin yaransu wajan basu ilimin addini da zamani domin ilmarta rayuwarsu domin ilimatar da ya mace guda daya tamkar ilmartar da al ‘ummace gaba daya.

Yayin zantawa da wasu daga iyayen yara da malamai, sun bayyana mana cewa rashin wadata da wasu daga cikin bukatu ne suka sa yaransu rashin zuwa makaranta.

Mai girma hakimi garin Ajingi yanuna farin cikinshi da wannan ziyara da wannan shirin yakawo karamar hukumar tasu, kuma yayi godiya da bangajiya da irin kai komo dangane da aiyukan shirin suke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *