Aisha Muhammad
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya nada malam Bala Ibrahim Mamser, a matsayin sabon Shugaban ma’iakatan gwamnatin Jihar.
Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannunĀ Shugaban maiakatan Jihar Alhaji Husaini Ali Kila.
Ta cikin sanarwar, nadin zai fara aiki nan take.
Kafin nadin na shi, Alhaji Mamser tsohon kwamishinan yada labarai da matasa ne na Jihar Jigawa.
Ka zalika gwamnan ya Kuma nada sanataĀ Mustapha Makama Kiyawa a matsayin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar.
Sai Alhaji Adamu Muhammad Garun Gabas a matsayin Shugaban makarantu masu zaman kansu na jihar.
Sauran nade-naden sun hada daĀ Abdullahi S.G Shehu a matasyin babban akantan naĀ JIhar sai kumaĀ Dr. Habib Muhammad Ubale.