A jiya hukumar Asusun Adashen Gata na Fansho na jiha da kuma kananan Hukumomin jihar Jigawa , ta kaddamar da biyan hakkokin maaikata na kudi fiye da naira miliyan dubu daya da miliyan dari biyu, da ashirin da biyar.
Rukunin maaikatan da za a biya hakkokin nasu sun hadar da maaikatan jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen ilmi da suka yi ritaya daga aiki su 411 da hakkokin magadan maaikatan da suka rasu a bakin aiki su 100 da cikon kudaden fansho ga masu karbar fanshon da suka rasu alhali basu cika shekaru biyar suna karbar fanshon ba su 37 da kuma cikon kaso takwas na kudaden asusun adashen gata ga maaikata biyu.
- SANATA IBRAHIM HASSAN HADEJIA YA KADDAMAR SHATIMA BEST BRAINS QUIZÂ
- Gabannin Zaben Fidda Gwani: Mataimakin Shugaban Kasa ya Tsallake Rijiya da Baya
A jawabinsa wajen kaddamar da biyan hakkokin maaikatan, sakataren zartarwa na Asusun Alhaji Kamilu Aliyu Musa yace hakkokin maaikatan da za a biya , sun hadar da naira miliyan dari tara da ashirin da dubu dari uku da talatin da daya da naira dari da sittin da tara a matsayin giratuti sai naira miliyan dari biyu da sittin da bakwai da dubu dari uku da ashirin da tara kudaden magadan maaikatan da suka rasu a bakin aiki sai miliyan 27 da dubu 952 cikon kudaden yan fanshon da suka rasu alhali basu cika shekaru biyar suna amsar fansho ba da kuma cikon kudaden asusun adashen gata ga mutane biyu naira 201,437.
Alhaji Kamilu Aliyu Musa yace a yanzu haka sun biya kudaden fansho na wannan watan kuma babu wani maaikaci da aka kawo file nasa ba a kammala aikinsa ba, dan haka ya yabawa gwamna Badaru Abubakar bisa hadin kai da goyan bayan da yake baiwa aiyukan asusun a kowane lokaci.
Ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga yan fanshon da ba a tantance ba dasu hanzarta zuwa domin a tantance su.
Wadanda suka karbi hakkokin nasu sun yabawa asusun bisa biyan hakkokin maaikata akan lokaci.