CITAD in the News

CITAD Ta Gabatar Da Sababbin Littattafan Da Ta Wallafa A Jami’ar Maiduguri

 

A cigaba da gabatar da littattafan da Cibiyar BunÆ™asa Fasahar Sadarwar da Cigaban Al’umma, CITAD, ta wallafa waÉ—anda su ka mayar da hankali akan yadda cin hanci da rashawa su ka dabaibaye É“angaren tsaron Æ™asar nan da kuma yadda kalaman Æ™iyayya kan haifar da tarzoma tare da Æ™ara rura wutar rikici a tsakankanin al’umma.

A jiya Litinin wakiliyar cibiyar ta CITAD, Malama Hassana I Waziri, Malama a sashen kimiyyar siyasa na jami’ar Maiduguri, ta gabatar da littattafan guda biyu a harabar jami’ar ta Maiduguri.

Littafi na farko mai suna The Compromised State: How Corruption Sustained Insecurity in Nigeria, wanda ya mayar da hankali akan yadda cin hanci da rashawa ya dabaibaye ɓangaren tsaron ƙasar nan aka kasa samo bakin zaren.

Sai kuma littafi na biyu mai suna Hate Speech: Discourse in Nigeria, wanda ya mayar da hankali akan yadda kalaman É“atanci su ke Æ™ara rura wutar rikici tare kuma da haifar da tarzoma a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *