CITAD in the News

Ƙarancin Mata A Harkokin Siyasar Najeriya: Cibiyar CITAD ta koka akan haka

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, ta koka akan yadda ake samun ƙarancin mata a harkokin mulki da ma siyasar Najeriya baki ɗaya.

Cibiyar ta CITAD ta bayyana takaicin na ta ne a yayin taron wata lakca da ta CITAD din ta shirya a dandalin intanet mai take ƙarancin mata a harkokin siyasar Najeriya, ina mafita? Wanda taron ya samu tallafin gidauniyar Rosa Luxembourg.

Malami a shashen nazarin halayyar ɗan adam a jami’ar Bayero da ke Kano, Dakta Aminu Ali ya ce akwai ƙarancin mata a harkokin siyasar kasar nan duk da irin ƙoƙarin da kungiyoyin fararen hula da na sa kai ke yi wajen ganin matan sun shiga an dama da su a harkokin siyasar.

Dakta Aminu Ali ya ce sakamakon tasirin al’ada da addini ya sanya mata su ke da ƙaranci a da’irar siyasar Najeriya, haka kuma ba a cika ganinsu ba a harkokin jama’a ko kuma ba su ragamar shugabancin al’umma ba.

A nata ɓangaren Uwargida Hamman Obels daga Cibiyar IRIAD cewa ta yi ya kamata a ɗauki wani mataki musamman idan aka zo batun rawar da mata za su iya takawa a harkokin siyasar Najeriya, domin tuni an bar mu a baya idan aka yi la’akari da sauran ƙasashen Afrika kamar su Rwanda da Tanzania da Senegal da kuma ƙasar Afrika ta Kudu.

Ta ƙara da cewa akwai abubuwa masu yawa da su ne su ka sabbaba rashin ganin matam a kujerun mulki, waɗanda su ka haɗa da al’ada da addini wanda ya haɗa da aure da kuma al’adar nan da wasu mutane ke kallon babu wani abu da mace za ta yi sai dai bauta a kasan Namiji da sunan aure.

Uwargida Hamman Obels, ta ƙara da cewa duk da cewa mata a Najeriya sun taka rawa sosai a ɓangaren tattalin arziki da kuma cigaba rayuwar al’umma amma har yanzu akwai masu daƙile cigaban matan tare da dankwafar da su a waje guda.

Haka kuma Hamman Obels din ta ce akwai buƙatar a samar da daidaito a tsakanin mata da maza musamman a harkokin mulki da siyasa domin hakan ne zai ƙara tabbatar da adalci.

A ƙarshe ta ce babu abin da zai samar da hakan sai an samu waɗanda za su rike hannun matan a harkokin siyasar kasar tare da wayar da kan al’umma akan siyasa ba mugun abu ba ce. Domin siyasa wani abu ce da ta ke da tasiri tare da taɓa rayuwar dukkanin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *