Daga: Asma’u Sa’id Hadejia
Sanatan Jigawa na arewa maso gabas sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya ziyarci bikin bude kaciki-kaciki ta “Shatima best Brains” wacca ya kirkira da nufin zaburar da dalibai dangane da ilimi tare da zakulo haziƙan dalibai tare da basu kyaututuka na musamman.
A yau ana gabatar da kashi na farko inda ake zaɓo dalibai da zasu gabatar da zagaye na karshe wanda za’ayi a gobe.
A na sa ran sanatan zai gabatar da tallafi na karatu a gobe, wannan dai na cikin kudirin sanatan na zakulo yaran marasa ƙarfi masu hazaƙa tare da ɗaukan nauyin karatun su.
A na sa ran mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma ɗan takarar gwamnan jihar Jigawa karkashin jam’iyyar APC zai kasance babban bako na musamman yayin rufe gasar.